Kwallon Kafa

Liverpool ta fara tattaunawa da kocin Swansea

'Yan wasan kungiyar Liverpool a Ingila
'Yan wasan kungiyar Liverpool a Ingila AFP

Rehotanni daga ingila na nuni da cewa kungiyar Liverpool tana gab da daukar kocin Swansea Brendan Rodgers matsayin sabon kocinta wanda zai gaji Kenny Dalglish da kungiyar ta sallama bayan kammala wasannin Premier a bana.

Talla

Rahotanni sun ce Liverpool ta gana da Brendan Rodgers bayan tattaunawa da kocin Wigan Roberto Martinez a makon jiya. An bayyana cewa Liverpool zata kulla yarjejeniyar shekru uku da Rodgers tare da biyansa kudi Fam Miliyan hudu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.