Tennis

Venus Williams ta fice French Open

Venus Williams 'Yar kasar Amurka ta nuna bacin rai bayan ta sha kashi hannun  Agnieszka Radwanska a gasar Roland Garros
Venus Williams 'Yar kasar Amurka ta nuna bacin rai bayan ta sha kashi hannun Agnieszka Radwanska a gasar Roland Garros REUTERS/Gonzalo Fuentes

Venus Willaims tsohuwar jarumar wasan Tennis ta Duniya ta fice gasar French Open ta Roland Garros bayan tasha kashi hannun Radwanka a zagaye na biyu. Amma Victoria Azarenka ta tsallake zagaye na gaba bayan ta lallasa Dina ‘Yar kasar Jamus.

Talla

A yau ne Maria Sharapova zata haska a zagaye na biyu.

A bangaren maza, Roger Federer da Novak Djokovic dukkaninsu sun tsallake, kuma Federer a jiya ne ya buga wasanni 234 a Frecnh Open ba tare da samun galabar shi ba bayan ya doke Adrian Ungur dan kasar Romania.

Djokovic mai rike da kofin Wimbledon da Us Open da Austalian Open ya doke dan kasar Slovenia ne Blaz Kavcic.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.