Tennis

Roger Federer ne zakara Wimbledon

Roger Federer yayin da ya saba kofin Wimbledon
Roger Federer yayin da ya saba kofin Wimbledon

A jiya lahadi Roger Federer na kasar Switzelland ya lashen kofin tennin na Wimbledon a karo na 7, hakan kuma na nuna yadda ya lalata mafarkin Andy Murray na Britaniya ke da shi na daga kofin na Wimbledon. Federer ya yi wa Murry ci 4-6, 7-5, 6-3, 6-4 wanda hakan ta bashi damar daukar kofin a karo na 7.jaridun kasar Britaniya na yau litinin sun ce duk da cewa Andy Murray ya gagara zaman dan Britaniya na farko tun shekarar 1936 da ya saba kofin na Wimbledon, amma fa bai gagara shiga zukatan ‘yan kasar ba.Jaridar Daily mail ta rawaito inda ya fashe da kuka bayan da ya gagara lashe gasar, inda wasu ‘yan kasar suka taya shi zub da hawaye.