Kwallon kafa

Bayern Munich za ta kai ziyara China

Wasu 'yan wasana kungiyar Bayern Munich
Wasu 'yan wasana kungiyar Bayern Munich Reuters

A karshen wannan watan na Yuli, kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich, ta kasar Jamus za ta je ziyara kasar Sin wato China, inda za ta buga wasanni 2. Wata sanarwar da kungiyar ta fitar, tace kungiyar za ta yi kwanaki 5 yayin wannan ziyarar, kuma a ranar 24 ga wata, za ta fara ne da karawa da kungiyar Beijing Guo da ke buga Chinese Super League.Ranar 26 su VfL Wolfsburg, da ita ma ke buga gasar Bundesliga.