Kwallon kafa

Ana zargin tsohon shugaban FIFA da karbar toshiyar baki

Wasu takardun kotu da aka fitar a kasar Switzerland sun nuna yadda tsohon shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, Joao Havelange ya karbi wasu makudan kudade a matsayin toshoiyar baki daga wani kamfani. Takardun sun ce Havelange mai shekaru 96, dan kasar Brazil, da kuma ya jagoranci FIFA tsawon shekaru 24, kafin Sepp Blatter ya maye gurbin shi a shekarar 1998, ya karbi kudin da saka kai franks na Swiss har miliyon daya da rabi.Dama an dade ana rade radin cewa yana da alaka da kamfanin mai suna International Sport and Leisure (ISL), da ke ayyuka tare da hadin gwiwar hukumar ta FIFA.