Kwallon Kafa

Chelsea da PSG sun yi Kunnen Doki a wasan zumunta

Wasu masoya bayan kungiyar PSG a harabar filin wasa na Yankee a kasar Amurka.
Wasu masoya bayan kungiyar PSG a harabar filin wasa na Yankee a kasar Amurka. REUTERS/Adam Hunger

Kungiyar Chelsea ta Ingila ta yi kunnen doki ci 1-1 da kungiyar PSG ta Faransa a wasan sada zumunci da kungiyoyin biyu suka buga a jiya Lahadi. A jiya ne kuma masoya Chelsea suka yi lale marhabin da tsohon jagoran Ingila John Terry wanda ya buga wasan farko tun bayan wanke shi daga zargin nuna wariyar launin fata.

Talla

Daruruwan masoya Chelsea ne suka yayata filin wasa domin karrrama John Terry lokacin da aka sako shi ana minti 63 da fara wasa.

Kungiyoyin biyu sun fafata ne a filin wasa na Yankee a kasar Amurka, kuma Carlo Ancelotti na PSG ya fafata ne tsakanin shi da tsoffin ‘yan wasan shi na Chelsea. ‘Yan wasan kasar Brazil ne suka zirawa kungiyoyin biyu kwallayensu a raga.

A daya bangaren kuma Liverpool ta yi kunnen doki ci 1-1 tsakaninta da FC Toronto, a wasan farko da Brendan Rodger ya jagoranci tawagar Liverpool a matsayin Koci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.