Kwallon Kafa

‘Yan Matan Amurka da Japan za su buga wasan karshe

'Yan Matan Amurka a lokacin da za su kara da 'Yan matan Faransa
'Yan Matan Amurka a lokacin da za su kara da 'Yan matan Faransa REUTERS/David Moir

‘Yan matan Amurka sun tsallake zuwa buga wasan karshe bayan samun nasarar doke ‘Yan matan Canada ci 4-3 fagen kwallon kafa a wasannin Olympics. ‘Yan matan amurka za su kara ne da ‘Yan matan Japan a wasan karshe bayan Japan ta lallasa Faransa ci 2-1.

Talla

An kammala miniti 90 na wasa ana ci 3-3, bayan karin lokaci ne Alex Morgan ta Amurka ta zira kwallo a ragar Canada a filin wasa na Old Trafford.

A ranar Alhamis ne ‘yan Matan Amurka zasu kara da ‘Yan matan Japan a wasan karshe a filin wasa na Wembley.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.