Kwallon Kafa

Yobo ya kulla yarjejeniya da Fenerbahce

Joseph Yobo Jagoran 'Yan wasan Super Eagle Na Najeriya
Joseph Yobo Jagoran 'Yan wasan Super Eagle Na Najeriya Ryan Pierse - FIFA/FIFA via Getty Images

Dan wasan Everton Joseph Yobo na Najeriya ya tabbatar da kammala kulla yarjejeniyar shekaru uku da kungiyar Fenerbahce. Yobo mai shekaru 31, ya kwashe kakar wasa biyu yana taka kwallo a kungiyar Fenerbahce a matsayin dan wasan aro. 

Talla

A shafin intanet na Everton, Joseph yobo ya mika godiyar shi ga kungiyar bayan cim ma yarjejeniya da Fenerbahce.

A shekarar 2002 ne Everton ta karbi Aron Yobo daga kungiyar Marseille ta Faransa, kuma ya bugawa Everton wasanni 250.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.