Olympics

Chris Hoy ya lashe zinari na 6 a Olympics

Dan tseren gudun keken Birtaniya Chris Hoy
Dan tseren gudun keken Birtaniya Chris Hoy Reuters/Paul Hanna

Dan wasan tseren keke Chris Hoy ya lashe zinari na Shida a wasannin Olympics, wanda kuma ya ba shi damar kasancewa mutum mai yawan lambobin yabo a tawagar Birtaniya. Dan kasar Jamus ne Maximilian Levy ya lashe Azurfa, sai kuma dan kasar New Zealnand Simon dad an kasar Holland Teun Mulder suka lashe Tagulla.

Talla

Usian Bolt na Jamica ya tsallake zuwa zagayen kusa da karshe a tseren gudun mita 200 tare da abokin gudun shi Yohan Blake.

A yau Laraba ne Usian Bolt da Yohan Blake zasu sake fafatawa a zagayen karshe, bayan bolt ya lashe Zinari, Blake kuma ya lashe Azurfa a tseren mita 100

‘Yar kasar Austalia kuma Sally Pearson ta lashe Zinari a tseren gudun mita 100 da ake tsallakar karfe. Kuma wannan ne Zinarin farko da kasar Australia ta lashe a wasannin tsalle sale da guje guje a London. ‘Yan kasar Amurka ne guda biyu suka lashe Azurfa da Tagulla.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.