Kwallon Kafa

Ingila ta doke Italiya, Argentina ta lallasa Jamus

'Yan wasan Ingila
'Yan wasan Ingila Reuters

A karon farko Ingila ta samu nasarar doke kasar Italia bayan kwashe shekaru 15 Italia na lallasata, kasar Spain kuma ta doke Puerto Rico 2-1, amma Jamus tasha kashi hannun Argentina a wasan sada zumunci da kasashen suka gudanar.

Talla

Kasashen kudancin Amurka guda biyu da suka kai ziyara Turai Argentina da Brazil, dukkaninsu sun lashe wasanninsu tsakaninsu da Jamus da kuma Sweden.

Ingila dai ta samu nasarar doke Italia ci 2-1. A karon farko tun nasarar da ingila ta samu a shekarar 1997.
Santi Cazorla da Cesc Fabregas ne suka zirawa Spain kwallayenta a ragar Puerto Rico.

A birnin Frankfurt Argentina ta lallasa Jamus ci 3-1, duk da cewa Lionel Messsi ya barar da bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Kasar Brazil kuma ta lallasa Sweden ne ci 3-0. Wasa tsakanin Faransa da Uruguay kuma an tashi ne babu ci. Belguim kuma ta doke Holland ci 4-2.

A wasannin kasashen Afrika, wasa tsakanin Cote d’Ivoire da Rasha an tashi ne kunnen doki ci 1-1, amma Zambia mai rike da kofin Nahiyar Afrika ta sha kashi hannun korea ta Kudu. Wasa tsakanin Ghana da China an tashi ne kunnen doki ci 1-1.

Wasa tsakanin Nijar da Najeriya kuma an tashi ne babu ci a birnin Yamai inda kasashen biyu ke shirye shirye wasannin neman shiga gasar cin kofin Nahiyar Afrika a watan Satumba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.