Premier

Manchester ta kammala cinikin Van Persie

Manchester United tace ta cim ma yarjejeniyar cinikin Robin Van Persie daga Arsenal kamar yadda sanarwar ta fito a shafin kungiyar. Yanzu ya rage a diba lafiyar dan wasan kafin kammala cinikin shi.

Robin Van Persie sanye da rigar  Arsenal
Robin Van Persie sanye da rigar Arsenal Reuters
Talla

Tuni dai Van Persie yace zai yi bankwana da Arsenal domin gurin shi bai yi dai dai da kungiyar ba kamar yadda Samir Nasri da Fabregas suka fice daga Emirate.

A kakar wasan bara Van Persie ya zira kwallaye 37 a raga, al’amarin da yasa aka zabe shi zakaran dan wasa a Ingila.

Babu dai sahihin bayani game da kudin cinikin dan wasan amma rahotanni na cewa Manchester ta saye dan wasan ne akan kudi da ake tunanin sun kai Fam Miliyan 20.

Idan dai har aka tantance Va Persie babu mamaki zai fara haskwa a wasa tsakanin Manchester da Everton a ranar Litinin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI