Premier

Chelsea ta doke Reading a Premier

Kungiyar Chelsea ta samu sa’ar doke Reading ci 4-2 a Premier League ta Ingila. Kafin zuwa hutun rabin lokaci a wasan, Reading ce ke kan gaba da ci 2-1, bayan dawowa ne Cahill ya samu sa’ar zirawa Chelsea kwallo ta biyu bayan Lampard ya zira kwallo ta farko.

Kwallon da Torres ya zira a ragar Reading yana barawon gida
Kwallon da Torres ya zira a ragar Reading yana barawon gida REUTERS/Toby Melville
Talla

Ana saura minti Tara a kammala wasan ne kuma Fernando Torres ya zira kwallo ta uku yana barawon gida. Ivanovic ne kuma ya zira kwallo ta hudu.

Yanzu Chelsea ce saman Teburin Premier da maki Shida, saboda ta buga wasa biyu. Wata kila jagorancin Teburin na iya zama na wuccin gadi kafin karshen mako sauran kungiyoyin su buga wasanninsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI