EUFA

Iniesta ya lashe kyautar gwarzon dan wasan Turai

Michel Platini Shugaban Hukumar EUFA tare da Andres Iniesta Gwarzon dan wasan Turai a bana
Michel Platini Shugaban Hukumar EUFA tare da Andres Iniesta Gwarzon dan wasan Turai a bana REUTERS/Eric Gaillard

Dan wasan Barcelona Andres Iniesta shi ne hukumar EUFA da ke kula da kwallon kafa a Turai ta zaba gwarzon dan wasanta bayan Dan wasan ya samu yawan kuri’u fiye da Cristiano Ronaldo da kuma abokin wasan shi Lionel Messi.

Talla

Gungun ‘Yana jaridun Turai ne guda 53 suka kada kuri’ar zaben dan wasan bayan kammala hada rukunin kungiyoyin da zasu kara da juna a gasar zakarun Turai a birnin Monaco.

Iniester ya lashe kyautar ne saboda irin rawar da ya taka a gasar cin kofin Turai wanda ya taimakawa kasar shi Spain lashe kofin gasar karo na biyu a jere.

Iniesta, mai shekaru 28, ya samu rinjayen kuri’u 19, yayin da kuma Ronaldo da Messi suka yi kunnen doki da juna da kuri’u 17.

Iniester yace ya sadaukar da wannan kyautar ga kungiyar shi Barcelona da kuma abokan wasan shi a Spain, bayan ya karbi kyautar daga hannun shugaban UEFA Michel Platini.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.