Kwallon kafa

Dubai ta nada Maradona a matsayin jakadan kwallon kafar kasar

Maradona
Maradona Reuters

Kasar Dubai ta nada Diego Maradona a matsayin jakadan kwallon kafar kasar, a wani kwantirakin shekara daya.  

Talla

Ana sa ran Maradona, dan shekaru 51, zai yi aiki haikan domin ganin cewa wasan kwallon kafar kasan ya bunkasa da basirarsa ta kwallon kafa.

“Mun tattauna da hukumar wasannin kasar Dubai akan yadda za a yi domin gano sababbin jinni a fagen wasan kwallon kafar kasar”, Maradona ya bayyana a wani taron manema labarai.
 

An dai sallami Maradona a matsayin mai horar da ‘Yan wasan club din Al Wasl, shekara daya bayan an nada shi saboda kasa ciyo kofin kakar wasan kasar.

Koda yake, ba a fadi nawa za a biya Maradona ba, amm kafofin yada labarai na ikrarin cewa kudin zai kai Dalar Amurka miliyan biyar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.