Tennis

Rauni ya fitar da Nadal daga gasar Davis Cup

Rafael Nadal
Rafael Nadal Reuters / Alessandro Bianchi

Shahararren dan wasan Tennis na uku a duniya, Rafael Nadal, ya fice daga gasar, Davis Cup a zagayen kusa da na karshe bayan ya samu rauni a gwiwarsa.

Talla

“Nadal ba zai buga wasa ban an da tsawon watanni biyu, zai kuma zauna ya huta don ya warke daga ciwon da ya samu a gwiwa” inji wani jami’I daga garinsu Nadal, Manacor Majora da ke Spain.

Nadal dai shi ne zakara mai ci a yanzu a gasar French Open, ya kuma fice net un bayan an doke shi a gasar Wimbledon a zagaye na biyu a watan Yuni bana.

“Lallai ina so na dawo bugawa wasa don na more wasan Tennis, ina da shekaru da dama a gaba kuma gwiwa ta na bukatar hutu” inji Nadal, dan shekaru 26.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.