Tseren kafa

Pistarious ya jawo muhawara akan tsayin kafar ‘Yan wasa

Dan tseren kafar kasar Afrika ta Kudu, Oscar Pistoriuos
Dan tseren kafar kasar Afrika ta Kudu, Oscar Pistoriuos REUTERS/David Gray

Dan wasan tseren kafar kasar Afrika ta Kudu, Oscar Pistorious, ya jawo mahawara akan gwargwadon da ya kamata tsayin kafar da ake karawa guragu masu wasanni ya kasance, da kuma ko ya ma da ce a dinga bari masu kafar karfen na shiga gasa.Pistorious a yanzu haka na shirin fuskantar kwamitin da ke shirya wasannin na gasar nakasassu domin ya gabatar da korafinsa na cewa kafar karfen wasu 'Yan wasan ya wuce kima.  

Talla

Wannan korafi na Pistorious, wanda ya kan yi tsere da masu lafiya, ya z one bayan ya fadi tseren mita 200 da ya shafe shekaru tara yana nasara akai.

A cewar Pistorious tsayin kafar da sauran ‘Yan wasa su ak yi amfani da shi ya wuce kima inda ya kara da cewa kafar dan wasan tseren Brazil, Alan Oliveira, wanda ya doke shi a ranar Lahadi ta yi tsayi da yawa.

Haka kuma, wanna korafi da Pistorious ya zo a dai dai lokacin da ake tantama ko tun a farko ya dace a dinga bari masu kafara karfe na karawa a gasar tsere kafa.

A da, wasu ‘Yan wasan tseren kafan masu lafiya, sun yi korafi akan cewa kafar karfen Pistorious na kara mai gudu inda shi Pistorious ya musa.

Amma a yanzu, Pistorious, na korafin tsayin kafar karfen na taimakawa wajen tseren.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.