Kwallon kafa

Wilshere zai dawo bugawa Arsenal wasa

Mai horar da 'Yan wasan club din Arsenal, Arsene Wenger, ya bayyana cewa mai yiwuwa, dan wasansa, Jack Wilshere, zai dawo buga wasa nan da wata daya.Wilshere ya dade bai bugawa club din ta Arsenal wasa ba tun farkon kakar wasa ta bara bayan fama da yake yi da wani ciwo a agararsa.  

Jack Wilshere
Jack Wilshere Wikipedia
Talla

Sai dai dan wasan ya fara halartar atiseyen club din ta Arsenal a kwana nan, kuma hakan inji Wenger, na nuna akwai yiwuwar cewa, Wilshere, zai fara buga wasa nan da farkon watan Oktoba mai zuwa.

Mutane da dama na ganin cewa, dawowan Wilshere zai karfafa club din ta Arsenal ganin cewa, Alex Song da Van Persie sun bar club din ta Arsenal.

Wenger ya kara da cewa, ba ya jin wata- wata a wannan kakar wasa inda ya kara da cewa lallasa club din Liverpool da su ka yi na nuna cewa club din na nan daram.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI