Kwallon kafa

Owen zai dawo buga wasa a Stoke City

Tsohon danwasan kwallon kafar kasar Birtaniya, Michael Owen, zai fara bugawa club din Stoke City, bayan watanni da dama da ya yi baya kwallo.A cikin yarjejeniyar da aka yi da Owen, zai bugawa Stoke City kwallo na tsawon shekara daya, za kuma a dinga biyansa ne a matakin duk wasan da ya buga. 

Michael Owen
Michael Owen Wikipedia
Talla

Michael Owen ya bugawa club din Liverpool, da Real Madrid kamin ya koma Manchester United inda daga nan yanzu kuma ya koma Stoke City wacce babbar abokiyar adawar club din Manchester United ce.
 

Owen shahararre ne a fagen zira kwallaye a raga inda a rayuwarsa ta kwallo ya zira kwallaye 221 a cikin wasanni 473 da ya buga.

Shi dai Owen, dan shekaru 32, ya sha fama da matsalar raunuka inda a kakar wasannin biyu da suka wuce wasa daya kacal ya buga.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI