Kwallon kafa

Bazan tankawa kalaman Ronaldo ba, inji Maurinho

Mai horar da 'Yan wasan Real Madrid, Jose Maurinho
Mai horar da 'Yan wasan Real Madrid, Jose Maurinho

Mai horar da ‘Yan wasan club din Real Madrid, Jose Maurinho, ya ki tankawa kalaman da dan wasansa, Cristiano Ronaldo, ya yi na cewa baya ya jin dadin zaman club din ta Real Madrid.Maurinho dai ya ce ba zai ce komai ba, a lokacin da ya ke amsa tambayoyin Jaridar Sports Daily da ke kasar ta Spain. 

Talla

A cewar Maurinho, zai iya Magana akan komai, amma banda batun Ronaldo, inda ma ya roki dan jaridar da kada ya tilasta mai yin Magana akan dan dan wasan.

Ronaldo dai bai nuna farin cikinsa ba bayan ya zira kwallaye biyu a ragar club din Granada a karawarsu da su ka yi a ranar lahadi, inda yin hakan ya ba mutane mamaki da yawa.

Da kuma aka tambayeshi mai yasa bai yi murna ba, sai ya ce baya farin ciki ne, inda ya kara da cewa rashin farin cikin nasa ba damuwa ba ce ta kansa.

Ronaldo har izuwa yanzu bai fito fili ya bayyana ko menen ke sa shi bakin ciki ba, sai dai ya fito shafin twitter, ya musanta zargin da ake yayatawa cewa batun kudi ne musabbabin rashin farin cikinsa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.