Kwallon kafa

An umurci ‘Yan wasan Ingila da kada sun raina Moldova

A yayin da za fara wasannin fidda gwanye na gasar cin kofin duniya a kasar Brazil, Kocin Ingila, Roy Hodgson, ya yi kira da ‘Yan wasansa da kada su raina ‘Yan wasan Moldova a karawar da za su yi a ranar Juma’a.Wasan dai za a buga shi na filin wasan Chisinau Zimbru a kasar ta Moldova.  

kocin Birtaniya, Roy Hodgson, a wani lokacin da ya ke ganawa da 'Yan wasan Birtaniya
kocin Birtaniya, Roy Hodgson, a wani lokacin da ya ke ganawa da 'Yan wasan Birtaniya REUTERS/Nigel Roddis
Talla

Wasan da Moldovan ta buga na karshe a wasanninta da Albania sun tashi kunnen doki ne.

‘Yan wasan na Birtaniya dai za su buga wasan ne ba tare da Wayne Rooney ba da Andy Carroll da kuma Andy Cole.

Hodgson ya kara da cewa, yana sane za su shiga wasan duk da cewa kasar ta Moldova ta yi kunnen doki da kuma shada kyar da su ka yi a wasansu da Holland.

Ya kara da cewa, idan har muka yi wasa muka yar da daman da muke da su wajen ganin cewa munyi bajinta, kusan yin hakan wawanci ne.

Mutane da dama suna ganin cewa, idan har kasar ta Ingila na so ta yi wani abun kirki a Brazil, dole ne ta fara nunawa duniya tun yanzu cewa tana da ‘Yan wasan kwarai.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI