US Open: Serena Williams ta shiga zagayen kusa da na karshe
‘Yar wasan Tennis din kasar Amurka, Serena Williams, ta samu shiga zagaye na karshe a gasar cin kofin US Open da ake gudanarwa a Amurka.
Wallafawa ranar:
Williams ta samu shiga zagayen a karo na hudu cikin shekaru biyar da su ka gabata, bayan ta doke Ana Ivanovic da ci 6-1 da ci 6-3 a cikin mintina 58.
‘Yar wasan Amurkan, wacce ta taba lashe gasar sau uku, kuma ta na da kambunan Grand Slam guda 14 za ta kara ne a ranar Juma’a a karon zagayen kusa da na karshe da ‘Yar kasar Italiya, Sara Errani.
“Na fito da karfi na ne, buga wasa da kwararriya kamar Ana, wacce da ta day ace a duniya, ya sa dole na fito da karfi na,” inji Williams a hirar da Kamfanin Dillancinlabaran AFP.
Williams ta kara da cewa, tana matukar farin cikin samun damar shiga zagayen na kusa da na karshe.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu