Kwallon kafa

Abidal zai dawo fagen wasa a watan Disamba bayan an yi mai dashen koda

Dan wasan kwallon kafar kasar Faransa dan kuma Club din Barcelona, Eric Abidal, zai dawo buga wasa bayan an yi nasarar yi mai dashen koda a watan Aprilun bana. Likitan da ya gudanar da aikin dashen kodar ne, Dokta Juan Carlos Garcia, ya bayyana hakan ga Kamfanin Dillancin labaran AFP. 

Eric Abidal
Eric Abidal www.google.fr
Talla

A watan jiya ne Abidal, Dan shekaru 32, ya bayyana cewa ya fara fita dakin motsa jinni ya kuma tabbatar cewa zai dawo fagen wasa a watan na Disamba.
 

“Babu damuwa idan har ya ce zai dawo filin wasa a watan na Disamba, ai bashi da wata matsala,” inji Dokta Garcia.
 

Ya kuma kara da cewa “Yanayin yadda abubuwa ke tafiya, matsalolin da zai fuskanta kadan ne, koda yake, ba za mu iya fadan abin da zai faru ba, amma komai na tafiya dai dai”
 

A farkon makon nan ne, mai horar da ‘Yan wasan na Barcelona, Tito Vilanova, ya saka sunan Abidal a cikin jerin sunayen ‘Yan wasa 25 da za su buga gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai, duk da cewa, Dan wasan, na kan murmurewa daga aikin da aka masa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI