Kwallon kafa

An cirewa Dan wasan Athletico Bilbao, Herrera kaba

'Yan wasan Bilbao a lokacin da suke murnan lashe wasan tsallakewa zuwa buga wasan karshe a Europa League
'Yan wasan Bilbao a lokacin da suke murnan lashe wasan tsallakewa zuwa buga wasan karshe a Europa League REUTERS/Felix Ordonez

Hukumar club din Athletico Bilbao da ke kasar Spain, ta bayyana cewa Dan wasan Club dinta mai buga tsakiya, Ander Herrera, ba zai buga wasa ba har na tsawon makwanni shida saboda wata tiyata da aka yi mai.

Talla

Dan shekaru, 23, Herrera, wanda ya yi ta fama da ciwon kaba, ya samu anyi mai tiyata a Birnin Munich, da ke Jamus an kuma yi nasara an cire masa ita.
 

Sai dai likitoci sun ce zai dauki akalla makwanni shida kamin ya fara buga wasa.

Likitocin sun kara da cewa, idan har aka yi aikin na kaba, yakan kai daga makwanni hudu zuwa makwanni shida kamin ya warke.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI