Wasan Dambe

Klitschko zai yi wasan kare kambunsa a birnin Moscow

Zakaran duniya a fagen wasan dambe Dan kuma kasar Ukraine, Vitali Klitschko, zai yi wasan kare kambunsa da Dan kasar Jamus din nan, wato Manuel Charr, a Birnin Moscow da ke kasar Rasha a ranar Asabar. Klitschko dan shekaru 40, a tarihinsa na wasan dambe ya samu nasarori 44 an kuma taba doke shi sau biyu.  

Vitali Klitschko Zakaran Damben Boxing  tare da dan uwansa Wladimir a fagen dambe kafin karawarsa da ya lashe kyautar ajin masu nauyi a karawarsa da dan kasar Poland Tomasz Adamek
Vitali Klitschko Zakaran Damben Boxing tare da dan uwansa Wladimir a fagen dambe kafin karawarsa da ya lashe kyautar ajin masu nauyi a karawarsa da dan kasar Poland Tomasz Adamek REUTERS/Peter Andrews
Talla

Shi ko Charr, wanda dan shekaru 27 ne, a tarhinsa na wasan dambe ya samu nasarori 21 kuma ba a taba doke shi ba.

Shi dai Klitschko ana mai ikrari da mai hanun karfe saboda basirar da Allah ya bashi ta iya doka.
 

“wannan wasa shi ne wasa na na farko a babban birnin Rasha, kuma ina mai farin cikin karawa a wasan kare kambuna,” inji Klitschko a wata hira da ya yi da ‘Yan jarida.
 

Akalla ‘Yan kallo kusan 30,000 ake sa ran zasu hallara a filin wasan Olimpisky a birnin na Moscow domin kallon wasan, a cewar Kamfanin Dillancin labaran AFP.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI