Paralympics

An kammala wasannin nakkasassu a London

An gudanar da bukin rufe gasar nakkasassu ta Paralympics a birnin London, bukin da mawaka irinsu Rihanna da Jay-Z suka cashe. An kwashe tsawon sa’o’i uku ana bukin rufe wasannin a filin wasa na Olympic mai daukar ‘yan kallo 80,000.

'Yan Wasan Paralympics ta nakkasassu
'Yan Wasan Paralympics ta nakkasassu Channel 4
Talla

Shugabannin gudanar da wasannin da suka gabatar da jawabi sun yaba da yadda aka gabatar da wasannin a London suna masu cewa a bana ne aka gudanar da wasanni mafi girma shekaru 52 da farawa.

Shugaban wasannin a London Sabastian yace tikitin shiga wasannin Miliyan Biyu da dubu dari bakwai suka sayar.

Kasar China ce ke da yawan lambobin yabo inda ta samu Zinari 95 Azurfa 71 sai kuma Tagulla 65, wanda ya ba China jimillar lambobin yabo 231.

Kasar Rasha ce a matsayi na biyu da jimilla lambobin yabo 102.

Sai Birtaniya mai masaukin baki a matsayin na uku da lambobin yabo 120. Rasha dai ta kasance ta biyu ne saboda tseren zinari biyu tsakaninta da Birtaniya.
Faransa ce a matsayi na 16. Da yawan lambobin yabo 45.

London 2012: Wasannin Olympic

A Nahiyar Afrika kuma kasar Africa ta Kudu ce a matasayi na daya da jimillar lambobin yabo 42. Amma ta 18 a jerin kasashen da suka shiga gasar.

Najeriya ce a matsayi na biyu a Afrika da lambobin yabo 13 amma kasa ta 22 a teburin lambobin yabon.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI