Kwallon kafa

Dalilin da ya sa ban gayyaci Crouch wasanmu da Ukraine ba – Inji Hodgson

Mai horar da ‘Yan wasan Ingila, Roy Hodgson, ya bayyana cewa dalilin da ya sa bai gayyaci Peter Crouch, cikin ‘Yan wasan da za su kara da kasar Ukraine ba, shine saboda dan wasan ya yi biris da shi a lokacin da ya saka sunansa a cikin ‘Yan wasan da za su buga gasar cin kofin nahiyar Turai a farkon shekarar nan. 

Mai horar da 'Yan wasan Ingila, Roy Hodgson
Mai horar da 'Yan wasan Ingila, Roy Hodgson www.google.fr
Talla

Shi dai Crouch, dan shekaru 31, ya dade ya na korafin cewa idan an kirashi ya bugawa kasarsa kwallo, ba a saka shi cikin zaratan ‘Yan wasan na farko, wanda hakan ba ya mai dadi.

Crouch a yanzu haka na da tarihin zira kwallaye 22 a wasanni 42 a club dinsa wanda hakan ya sa shi ya zama dan kasar Biraniya na 16 a cikin wadanda su ka fi cin kwallaye a kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI