Kwallon kafa

An jibge jami’an tsaro a ofishin hukumar kwallon kafar Kamaru

An jibge jami’an tsaro a ofishin hukumar kwallon kafar kasar Kamaru da ke Yaounde, bayan wasu masoya kwallon kafa a kasar sun yi barazanar kai hari akan ofishin hukumar saboda kashi da kasar ta Kamaru ta sha a hanun kasar Cape Verde.

Dan wasan kasar Kamaru, Samuel Eto
Dan wasan kasar Kamaru, Samuel Eto REUTERS/Jerry Lampen
Talla

Ita dai kasar Cape Verde, ta lallasa Kamaru ci biyu ba kodaya a wasannin fidda gwanayen da za su halarci gasar cin kofin nahiyar Afrika.

Hakan ya sa ‘Yan kasar ta Kamaru, su ka yi wata zanga zanga a kofar ofishin hukumar kwallon kafan, wanda hakan ya sa aka jibge jami’an tsaro a ofishin.

Wani makwabcin ofishin hukumar kwallon kafar, mai suna, Martin Ndzinga, ya fadawa Kamfanin Dillancin labaran AFP cewa, idan mutum ya ga irin jami’an da aka jibge a kofar ofishin sai ya dauka ana yaki ne a kasar.

Ita dai kasar Kamaru, sau hudu ta na lashe kofin gasar ta nahiyar Afrika, ita ce kuma kasa daga nahiyar Afrika ta farko da ta taba kaiwa zagayen wasan kusa da na kusa da na karshe, wato Quarter Finals, a gasar cin kofin duniya.

Kuma a yanzu haka kasar ta na fuskantar barazanar rashin samun damar zuwa gasar ta cin kofin nahiyar Afrika.

Koda yake mai horar da yan wasan kasar Denis Lavagne, ya tabbatar da cewa babu damuwa kasar za ta samu nasarar zuwa gasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI