Tennis

Murray ya lashe US Open bayan doke Djokovic

Andy Murray na Birtaniya ya lashe kofin gasar US Open bayan doke Novak Djokovic na Serbia a wasan karshe. Andy Murray dai ya kafa tarihi ne a mtasayin mutum na farko daga Birtaniya wanda lashe kofin gasar US open bayan kwashe shekaru 76, Tun bayan Fred Perry wanda ya lashe gasar a shekarar 1936.

Andy Murray yana sunbatar kofin da ya lashe a gasar US Open bayan doke Novak Djokovic a wasan karshe
Andy Murray yana sunbatar kofin da ya lashe a gasar US Open bayan doke Novak Djokovic a wasan karshe REUTERS/Adam Hunger
Talla

Murray shi ne ya lashe kyautar Zinari a wasannin Olympics, kuma Novak Djokovic wanda shi ne na daya a duniya ya amsa shan kaye.

Sai dai Andy Murray yace har yanzu Roger Federer da Novak Djokovic suna gaban shi a fagen Tennis.

Domin kofi 29 cikin Talatin, Federer da Djokovic da Rafael Nadal ne suka raba kofunan a tsakaninsu.

Sau hudu ne dai Murray ya ke shan kashi hannun Roger Federer a wasan karshe na manyan gasar Tennis. Gasar US Open a shekakarar 2008 da Australian Open a shekarar 2010 sai kuma a bana da ya sha kashi hannun Federer a Wimbledon.

Don haka Andy Murray yace yana da wahala ya yi gogayya da su a matsayin Jarumin Tennis na duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI