Kwallon kafa

Capello ya yi farin cikin lashe wasannin farko, amma ya ce da sauran rina a kaba

Mai horar da ‘Yan wasan club din kasar Rasha, Fabio Capello, ya nuna farin cikinsa da nasarorin da kasar ta Rasha ta samu a wasanninta na farko a yayin da aka buga wasannin fidda gwanayen da za su halarci gasar cin kofin duniya.

Mai horar da 'Yan wasan kasar Rasha, Fabio Capello
Mai horar da 'Yan wasan kasar Rasha, Fabio Capello REUTERS/Nigel Roddis
Talla

A wasannin da ta buga, kasar ta Rasha ta dai ta doke kasar Isra’ila da ci hudu ba ko daya, sannan kuma ta doke kasar Northern Ireland da ci biyu ba ko daya.

Sai dai Capello ya kara da cewa akwai sauran jan aiki a gaba, musamman ma indan aka yi la’akkari da cewa uku daga cikin ‘Yan wasansa sun samu rauni.

A dai watan da ya gabata ne, Capello ya zama Coach din club din kasar ta Rasha.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI