Kungiyoyi 23 sun fuskanci fushin EUFA
Hukumar EUFA da ke kula da kwallon kafa a Nahiyar Turai ta sanya takunkumin dakatar da bada kudi ga wasu kungiyoyin kwallon kafa 23 da suka ki bin dokokinta. Kungiyoyin kuma sun hada da Atletico Madrid, Kungiyar da ta lashe kofin gasar Europa league da Malaga a Spain da kuma Sporting da Fenerbahce ta Turkiya wadanda yanzu haka aka kaddamar da bincike akansu.
Wallafawa ranar:
Kungiyoyin kwallon kafar na fuskantar bincike ne, saboda rashin biyan kudade ga ma'aikata tare da rashin biyan haraji ga hukumomi a kan lokaci.
Hukumar EUFA ta bai wa kungiyoyin su 23 wa'adi daga nan zuwa ranar 30 ga watan Satumba, domin gabatar da bayani ga hukumar ba su da matsalar kudade.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu