Cameron ya ba iyalan wadanda su ka mutu hakuri a filin wasan Liverpool shekaru 23 da su ka gabata
Firaministan kasar Birtaniya, David Cameron, ya fito ya bawa iyalan wadanda su ka mutu a cuncurundon filin wasa shekaru 23 da su ka gabata hakuri a lokacin da club din Liverpool ke wasa.
Wallafawa ranar:
Cameron ya kara da cewa bayan da ‘Yan sanda su boye shi ne ya sa ake ganin laifin magoya bayan club din Liverpool ne, inda ya kara da cewa ba a musu adalci ba.
Akalla mutane 96 su ka mutu a wani cuncurundo daya auku a filin wasa, a yayin da Liverpool ke buga wasa a shekarar 1989, wanda aka dora laifin akan magoaya bayan club din.
Haka shi ma Editan jaridar The Sun da ke kasar Birtaniyar, Kelvin Mackenzie, ya fito ya nema gafara saboda labarin daya buga akan lamarin
Amma wasu bayanai da aka fito da su a kwana kwanan nan sun nuna cewa, ‘Yan sanda sun boye ainihin bayanai akan abin da ya faru a lokacin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu