Kwallon kafa

An soki FIFA akan yawan wasannin kasa da kasa

Tambarin hukumar FIFA
Tambarin hukumar FIFA Reuters

Shugaban club din Bayern Munich, Uli Hoeness, ya soki hukumar kwallon kafar duniya, wato FIFA akan buga wasanni na kasa da kasa da ake ta yi a lokaci daya, wanda hakan kuma ya yi kicibis da farkon kakar wasa ta bana.

Talla

A cewar Hoeness, abin mamaki ne a ce a wasanni biyu kawai suka buga a yayin da aka shiga tsakiyar watan Satumba.

Shima dai daya daga cikin shugabanin club din ta Bayern, Karl Heinz Rummernigge, ya yi irin wannan suka a ‘yan kwanakin nan inda ya ce, taswirar wasanni da hukumar ta FIFA ta tsara a wannan shekarar bai yi tsari ba, wanda hakan ya jawo muhawara.

Kasar Jamus dai ta sha kayi da ci 3 da daya a lokacin da ta kara da kasar Argentina a wani wasan sada zamunci a tsakiyan watan Agusta.

Sannan kuma ta sake karawa da kasashen Faroe Island da kuma Austria a satin da ya gabata.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.