Wasanni

An dage takunkumi kan Meng ‘Yar tseren daben santsi a kasar Sin

Shahararren ‘Yar wasan tseren daben santsin kasar Sin din nan, Wang Meng, za ta dawo karawa a fagen wasan tsere bayan an dage wani takunkumi da ya hanata yin gasa ma kasarta na tsawon watanni 13.

'Yar wasan tseren daben santsin kasar Sin
'Yar wasan tseren daben santsin kasar Sin www.whatsonxiamen.com
Talla

Ita dai Meng, ‘Yar shekaru 27, wacce kuma keda lambobin yabo da ta samu a wasannin Olympic guda hudu, ta yi fada ne da manajanta don ya mata fada akan ta dawo masaukin ‘Yan wasan kasar ta Sin a latti.

Wannan dai bashi ne karo na farko da Meng ke fada da manyan hukumar wasannin kasar ba, domin a shekarar 2007 an taba korarta daga cikin ‘Yan wasan kasar Sin na tsawon watanni shida bayan ta yi suka da yadda kocinta ke horar dasu.

Dawowar Meng, karawa a fagen tsere na nufin za ta wakilici kasarta a gasar wasannin da za a yi a kasar Rasha a shekarar 2014.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI