FIFA ta fitar da sunan naman dajin da za ayi amfani da shi a gasar cin kofin duniya na shekarar 2014
Hukumar kwallon kafa ta duniya, wato FIFA ta fitar da sunan naman dajin da za a yi amfani da shi a matsayin alamar gasar cin kofin duniya da za a gudanar a shekarar 2014 a kasar Brazil.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
A cewar hukumar an zabi naman dajin da ake kira Armadillo, wanda aka fi samu a yankin Kudancin Amurka, wanda kuma ke da kamanni da damo, sai dai yana da baki mai tsawo kamar na Alade da kuma koko a baya kamar na kunkuru.
Shi dai Armadillo na daya daga cikin namun dajin da ke fuskantar barazanar gushewa daga doron kasa, a kuma cewar Babban Sakataren hukumar ta FIFA, Jerome Valcke, an zabi wannan naman dajin ne saboda a fadakar da mutane akan muhimmancin muhalli da kuma kare halattun duniya.
Idan dai za a tuna, a gasar cin kofin duniya da aka buga a kasar Afrika ta kudu a shekarar 2010, an yi amfani ne da zanen Damisa a matsayin alamar gasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu