Wasanni
Japan ta janye daga wasannin Sin
Kasar Japan ta janye daga shirinta na halartar gasar wasan tseren keke da wasan Table Tennis da za a gudanar a kasar Sin. Hukumar wasanni kasar Japan ce ta fadawa Kamfanin Dillancin labarai na AFP cewa, ta janye daga halartar gasar saboda gudun kada a kai ma ‘Yan wasanta hari ganin takadamar da ke tsakanin kasashen biyu akan wasu tsibirrai.
Wallafawa ranar:
Talla
Tun a makon da ya gabata ne, ake ta yin zanga zangar nuna kin jinin kasar Japan A kasar Sin, akan wasu tsibirai da kasashen biyu ke ikrarin mallakansu ne.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu