Tseren Keke

An bawa Qatara damar gudanar da gasar tseren keken duniya na shekara ta 2016

Wani dan wasan tseren keke
Wani dan wasan tseren keke REUTERS/Denis Balibouse

An bawa kasar Qatar damar daukan bakuncin gasar tseren keke ta duniya da za a gudanar a shekarar 2016. Hukumar tseren keke ta duniya, wato UCI ce, ta sanar da hakan bayan wani taro da aka gudanar.  

Talla

A shekara mai zuwa dai kasar Italiya ce za ta dauki bakuncin gasara a birnin Florence, a yayin da kasar Spain za ta daukin bakuncin gasar a shekarar 2014 a birnin Ponferreda, kana birnin Richmond da ke Jihar Virginia a kasar Amurka zai dauki bakuncin gasar a shekarar 2015.

Ita dai kasar ta Qatar it ace har ila yau za ta dauki bakuncin gasar cin kofin duniya na kwallon kafa a shekarar 2022, kana ita ce za ta dauki bakuncin gasar wasan ninkaya, wato Swimming na duniya a shekarar 2014, a yayin da a shekarar 2014 za ta dauki nauyin gudanar da gasar Handball na duniya a bangaren maza.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI