Kwallon kafa

Kocin Chelsea, Matteo ya koka da raunin Oscar

Kocin Club din Chelsea, Roberto Di Matteo, ya bayyana cewa bashi da tabbacin ko dan wasansa, Oscar zai samu buga wasansu da za su buga da club din Stoke a ranar Asabar.

Kocin Chelsea, Roberto Di Matteo
Kocin Chelsea, Roberto Di Matteo static.guim.co.uk
Talla

Wannan sanarwar ta biyo bayan ciwo da Oscar ya samu ne a agararsa, a lokacin da club din ta Chelsea ta ke fafatawa da club din Juventus a jiya , inda club din su ka zira kwallaye bi biyuwa junansu.

Kuma Oscar,wanda ainihin dan wasan kasar Brazil ne, ya ci ma Chelsea kwallaye a wasan.

A yanzu haka dai, kocin na Chelsea na neman hukumar ta UEFA da ta sake duba irin shigar karfi da dan wasan Juventus, Arturo Vidal ya yiwa Oscar, wanda ya yi sanadiyar jin ciwonsa, domin a yi mai hukunci.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI