Kwallon kafa

Masu kallon wasan kwallon kafa sun karu a China saboda Drogba

Didier Drogba
Didier Drogba Reuters

Wani bincike da Jaridar nan da ake kira Oriental Morning Post ta gudanar, ta gano cewa yawan mutanen da ke zuwa kallon wasan kwallon kafa a gasar Chinese Super League sun karu daga dubu goma sha biyar zuwa kusan dubu 20, bayan dan wasan kasar Cote d’Ivoire nan, wato, Didier Drogba, ya fara bugawa club din Shanghai Shenhua wasa. 

Talla

Idan za a iya tunawa, a tsakiyar watan Yuli ne Drogba ya koma Club din Shenghai Shenhua, inda rahotanni su ka ce ana biyansa kudi dalar Amurka sama da 300,000, a sati.
 

Wannan bincike an yi shi ne a dai dai lokacin da zaman Drogba ke fuskantar barazana a club din ta Shenghai Shenhua saboda takaddama da ake fama da ita akan kasafin kudi, koda yake Drogba ya ce babu inda zai je ya na nan daram a club din ta Shenghai Shenhua.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.