Kwallon kafa

Messi na cigaba da tserewa Ronaldo da yawan kwallaye

Dan wasan Barcelona Lionel Messi (dama) yana gaisawa da Cristiano Ronaldo a bukin bada kyautar gwarzon dan wasan Duniya
Dan wasan Barcelona Lionel Messi (dama) yana gaisawa da Cristiano Ronaldo a bukin bada kyautar gwarzon dan wasan Duniya

Dan wasan Barcelona, Lionel Messi na cigaba da tserewa Cristiano Ronaldo, Dan wasan Real Madrid, da yawan kwallaye a wasannin da ake bugawa. Messi dai ya zira kwallaye biyu daga cikin kwallaye uku da club din Barcelona ta saka a ragar Spartak Moscow a karawar du su ka yi a shekaran jiya.  

Talla

Shi ma dai Ronaldo ya zira kwallo daya a cikin kwallaye uku da Real Madrid ta saka a wasansu da Manchester City wacce ta sha kayi a karshen wasan da ci 3-2.

Messi wanda shine ke rike da kambun gwarzon dan wasan kwallon kafar duniya a shekaru uku da su ka gabata, na da kwallaye 53 a cikin wasannin guda 69 da ya buga a gasar Champions League.

Shi kuwa Ronaldo a yanzu haka na da kwallaye 39 a cikin wasanni 81 da ya buga.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.