Kwallon kafa

Ya kamata a mayar da gaisuwa zabi ga ‘Yan wasa - Fernades

Mai club din Queen’s Park Rangers, Tony Fernades, ya bada shawarar cewa ya kamata a mayar da gaisuwa ta musafaha da ‘Yan wasa ke yi kamin a fara wasa ta zamanto ba dole ba. Fernandes ya bada shawarar ne bayan, Dan wasan Queen’s Park Rangers, Anton Ferdinand ya share, wato ya ki gaisawa da ‘Yan wasan Chelsea, John Terry da kuma Ashley Cole a wasan da su ka buga wanda aka tashi ba ci kodaya. 

'Yan wasa na musfaha kamin a fara wasa
'Yan wasa na musfaha kamin a fara wasa static.guim.co.uk
Talla

Haka shima kyfatin din club ta Queens Park Rangers, wato, Park Ji Sung ya ki gaisawa da Terry, a yayin da Terrin ya mika mai hanu.

Wannan takaddama dai ta samo asali ne tun a watan Oktoban bara inda Ferdinand ya zargi John Terry da amfani da kalaman wariyar launin fata a lokacin da su ka sami sabani.

Koda yake, wata kotu ta wanke John Terry daga wannan zargi, a yayin da hukumar FA ta ke nata bincike akan zargin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI