Kwallon kafa

An dage wasan Real da Vallecano saboda rashin wuta

A jiya Lahadi aka dage fafatawar da za a yi tsakanin club din Real Madrid da kuma Rayo Vallecano bayan wasu dab a asan ko su waye sun bata fitulun filin da za a gudanar da wasan. Shugaban club din Rayo ne , Raul Martin Pres, ya bayyana bacin fitulun a jiya.  

Yadda filin Vallecas ya kasance da duhu bayan an bata fitulun filin wanda Madrid da Rayo za su fafata
Yadda filin Vallecas ya kasance da duhu bayan an bata fitulun filin wanda Madrid da Rayo za su fafata REUTERS/Susana Vera
Talla

A yanzu haka dai za a buga wasan a yau Litinin, a wasan wanda Rayo za ta karbi bakuncin Madrid a filin wasanta da ake kira Estadio de Vallecas.

Pres ya kara da cewa, jami’an tsaro na nan na binciken wadanda da k da hanu a lamarin, inda ya kara da cewa wannan abin day a faru abin kunya ne da kuma takaici.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI