Kwallon kafa

John Terry ya yi ritaya daga buga kwallon kafa na kasa da kasa

Dan wasan club din Chelsea kuma har ila yau tsohon Kyfatin din kasar Ingila, John Terry ya yi ritaya daga buga wasan kasa kasa. Ba’a fadi dalilin da yasa dai John Terry ya yi ritaya ba sai dai wannan ritaya ta shi ta zo, sa’oi kadan kamin hukumar kwallon kafar kasar ta fara sauraren bayanai akan zargin Terry da ake yi, na yin amfani da kalaman wariyar launin fata a lokacin da su ka samu sabani tsakannnnninsa da Dan wasan Queen’s Park Rangers, wato Anton Ferdinand. 

John Terry.
John Terry. REUTERS/Stefan Wermuth
Talla

Dan shekaru 31, John Terry, a cewar wasu jaridun kasar Ingila, ya kasance dan wasan kwallon kafa da ya fi shiga rikici a kasar ta Ingila, inda aka alakanta shi da yin fada a wuraren shakatawa da kuma neman buduruwar abokinsa day a taba yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI