Wasan Dambe

‘Yan fashi sun kashe tsohon zakaran damben kasar Afrika ta Kudu

Cornelius Sanders
Cornelius Sanders i.ytimg.com

‘Yan fashi a kasar Afrika ta Kudu sun kashe tsohon zakaran damben kasar, Cornelius Sanders, bayan sun harbe shi a wani taron bikin murnar shekaru 21 da wani dan Dan uwansa ya yi. Sanders dan shekaru 46, an harbe shi ne a hanu da kuma ciki a loacin da ‘Yan fashin su ka mamaye wani wurin cin abinci inda Sanders ke yin bikin tare da sauran iyalansa.  

Talla

An dai garzaya da Sanders zuwa asibiti bayan harbi sai dai a sanyin safiyar Lahadi ya cika.

Sanders, wanda ake wa lakabi da “The Sniper” saboda iya duka da hanunsa na hagu, ya taba lashe kambun zakaran duniya na dambe a shekarar 2003, a lokacin da ya yiwa Vladimir Klitschko, dan kasar Ukraine dukan faraddaya.

A tarihinsa na dambe ya yi wasa sau 46 an kuma doke shi sau hudu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI