Tennis

Bani da ranar dawowa wasa, inji Rafael Nadal

Dan wasan Tennis din kasar Spain, Rafael Nadal
Dan wasan Tennis din kasar Spain, Rafael Nadal REUTERS/Toby Melville

Sharararren dan wasan Tennis kuma dan kasar Spain, Rafael Nadal, ya ce a yanzu haka babu ranar da zai dawo buga wasan Tennis, kusan watanni uku bayan ya fice daga gasar Wimbledon bayan ya samu rauni. Rafael, wanda ya bayyana hakan a wata hirarsa da ‘Yan jarida, ya ce hasali ma, tun daya fice daga gasar bai rike abin buga Tennis ba. 

Talla

A yanzu haka dai Rafael na kan murmurewa daga raunin da ya ji a gwiwarsa ta hagu, shine kuma dan wasan Tennis na biyu a duniya inda ya lashe gasar Grand Slams 11 bayan abokin hamayyrasa, Roger Federer, wanda shi kuma ya lashe gasar Grand Slams 17.

A yayin da David Ferrer ke ganawa da 'Yan jarida, wanda shima fitacce a gasar Tennis daga kasar Spain, ya ce idan Nadal ya dawo, zai dawo daga karfinsa, kuma zai iya buge abokin hamayyarsa, Roger Federer.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.