Kwallon kafa

Najeriya ta lallasa Azerbaijan 11-0

'Yan wasan Najeriya yan kasa da shekaru 17 (Flamingos) suna murnar zira kwallo
'Yan wasan Najeriya yan kasa da shekaru 17 (Flamingos) suna murnar zira kwallo img.naij.com

A fagen gasar kwallon kafa na mata kuma na ‘Yan kasa da shekaru 17, wanda ake gudanarwa a kasar Azerbaijan, a jiya ‘Yan wasan Najeriya, wato Flamingos, sun samu gagarumar nasara akan kasar ta Azerbaijan, inda suka zira kwallaye 11 a ragar Azerbaijan.

Talla

Tun a cikin mintina biyar na farko a kuma zagayen na farko, Najeriya ta zira kwallaye bakwai, inda Chinwendu Ihezuo ta fara zira kwallon farko, ta kuma kara guda hudu daga baya, wanda a yanzu hakan ya bata damar zama wacce ta fi kowa yawan kwallaye a gasar.

Sannan, Halimatu Ayinde da Tessy Biaho suka zira kwallaye bi biyu daga baya.

A yanzu haka, ‘Yan wasan Flamingos, za su kara ne da kasar Colombia a ranar Asabar a wasansu na gaba, sune kuma ke saman teburin rukuninsu da maki hudu.

A wani bangare kuma, kasar Amurka ta doke kasar Gambia da ci 6-0.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI