Za a fara horar da matasa a fagen wasan damben Ghana
Wata kungiya mai zamankanta, a kasar Ghana, ta shirya wata horarwa ga matasa masu sha’awan damben zamani, a irin kokarinta na ganin cewa ta farfado da wasan dambe a kasar. A cewar shugaban kungiyar, Atta Lartey, horarwar za ta hada matasa wadanda ke tsakanin shekaru 12 ne zuwa 16.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Ya kara da cewa a irin wannan horarwarce aka lalubo shahararren dan wasan damben duniya, Joseph Agbeko, wanda aka fi sani da King Kong, wanda kuma dan kasar Ghana ne.
A cewar kungiyar, gudanar da horarwar zai taimaka wajen maye gurbin da tsofaffin ‘Yan dambe na kasar su ka bari, kuma ya lalubo sabbin ‘Yan wasan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu