Kwallon kafa

Rooney ya dawo daga jinya

Dan wasan Manchester United, Wayne Rooney, ya dawo bugawa club dinsa wasa bayan ya samu sauki daga raunin da ya samu a watan Agustan bana, inda ya buga wasansa na farko tsakaninsu da club din Newcastle, a gasar English League Cup wanda su ka yi nasara da ci 2-1.

Wayne Rooney Dan wasan  Manchester United
Wayne Rooney Dan wasan Manchester United Reuters
Talla

Rooney wanda dan wasan kasar Ingila ne kuma dan shekaru 26, ya samu rauni ne a wasansu da Fulham a watan Agusta inda jinni ya dinga kwarara a kusa da mararsa.

Watan shi dai daya baya buga wasa, inda ya rasa buga wasanni hudu, an kuma saka shi ne a wasan nasu da Newcastle a cikin minti na 76.

Rooney ya kuma rasa buga wasa na kasa da kasa guda biyu, inda ya nuna matukar farin cikinsa na dawo kwallo bayan ya warke.

Wata takaddama da Mai horar da ‘Yan wasan zai fuskanta, wato Alex Ferguson, ita ce wanda zai ajiye a tsakanin Robin Van Persie da Shinji Kagawa domin Rooney ya koma wurinsa a wasan da Manchester United za ta buga da Tottenham a cigaba da gasar Premier League a ranar Asabar.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI