Kwallon kafa

Tsohon mai horar da ‘Yan wasan Man City, John Bond ya rasu

Marigayi, tsohon mai horar da 'Yan wasan Manchester City
Marigayi, tsohon mai horar da 'Yan wasan Manchester City www.pinkun.com

Tsohon mai horar da ‘Yan wasan club din Manchester City, wanda kuma ya buga wasannin 400 a club din West Ham United, wato John Bond ya rasu. 

Talla

Bond ya rasu ne yana dan shekaru 79, shi ne kuma ya jagaoranci Manchester City a shekarar 1981, inda ta lashe FA Cup, a lokacin da su ka buga da Tottenham Hotspur.

Ya kuma taba horar da club din Norwich City da Burnley da kuma club din Swansea City.

Bond ya mutu ya bar Da daya, Kevin Bond, wanda ya taba buga wasa a karshin mahaifinsa a club din ta Manchester City.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.