Kwallon kafa

An nemi Terry da ya rungumi kaddara, a yayin da Maurinho ya mara mai baya

Tsohon mai horar da club din Chelsea kuma mai horar da Real Madrid, José Mourinho
Tsohon mai horar da club din Chelsea kuma mai horar da Real Madrid, José Mourinho Lars Baron/Bongarts/Getty Images

Tsohon mai horar da ‘Yan wasan Ingila, Graham Taylor, ya yi kira ga dan wasan Chelsea, John Terry, da ya amince da hukuncin da aka yanke mai dake cewa ba zai buga wasanni hudu ba, bayan an same shi da laifin yin amfani da kalaman batanci da nuna wariyar launin fata ga dan wasan Queen’s Park Rangers, wato Anton Ferdinand.  

Talla

A jiya ne Hukumar Kwallon Kafa ta Ingila ta yankewa Terry wannan hukunci inda har ila yau aka ci taransa na kudin Euro 220,000, a yayin da shi Terry a yanzu haka na da kwanaki 14 na damar ya daukaka kara akan wannan hukunci.

Sai dai tsohon mai horar da ‘Yan wasan Chelsea, Jose Maurinho, ya fito ya kare Dan wasan, inda ya bayyana cewa sam, Terry ba mutum ne mai nuna wariyar launin fata ba.

Maurinho dai ya taba horar da Terry a club din ta Chelsea daga shekarar 2004 zuwa 2007.

A kuma cewar Maurinho, a lokacin da ya ke horar da club din ta Chelsea, akwai ‘Yan wasa daga nahiyar Afrika mutum 12, kuma a lokacin, Terry na da kyakyawan danganta da wadannan ‘Yan Wasa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.