Wasan Tennis

Murray na hanyarsa ta lashe gasar Japan Open

Andy Murray
Andy Murray

Dan wasan Tennis na daya a duniya, Andy Murray, na kan hanyarsa ta sake lashe gasar Japan Open bayan ya doke Stanislas Wawrinka dan kasar Switzerland a zagaye na kusa da na kusa da na karshe, wanda hakan ya bashi damar shiga zagaye na kusa da na karshe, wato Semi finals ke nan.

Talla

Murray dai ya doke Wawrinka ne da ci 6-2, 3-6, da kuma 6-2, a gobe Asabar ne kuma zai kara da Milos Raonic dan kasar Canada, wanda shima ya sami nasarar doke Janko Tipsarevic da ci 6-7, 6-2, 7-6.

A kuma fagen gasar China Open, da ake gudanarwa Beijing, har ila yau a fagen wasan Tennis, a wasannin da aka buga dazu a zagaye na kusa da na kusa da na karshe, a bangaren mata, Victoria Azarenka ‘Yar kasar Belarus ta doke Romina Oprandi ‘Yar kasar Switzerland da ci 6-2, 6- da nema.

Maria Sharapova ‘Yar kasar Rasha ta lallasa Angelique Kerber ‘Yar kasar Jamus da maki 6- da nema, da kuma 3- da nema.

Li Na ‘Yar kasar China ta doke Agneiszka Radwanska ‘Yar kasar Poland da ci 6-4, 6-2.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI